Sinopsis
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.
Episodios
-
Rashin malamai ya tilasta iyaye janye yaransu daga makarantu a kudancin Najeriya
06/11/2024 Duración: 09minShirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda iyaye a yankin kudancin ƙasar ke janye yaransu daga Makarantu saboda ƙarancin makarantu a yankin. Jihar Abia na sahun ƴan gaba gaba da ke fama da wannan matsala inda a baya-bayan nan aka tarin yaran da suka daina zuwa makaranta.
-
Gwamnatin Bauchi na shirin mayar da yara fiye da miliyan 1 makarantu
29/10/2024 Duración: 09minShirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda gwamnatin jihar Bauchi a Najeriya ke yunƙurin mayar da yara fiye da miliyan guda makaranta a wani yanayi da ake ganin ƙaruwar yaran da basa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar. Tuni masu ruwa da tsaki a wannan yanki suka yi maraba da matakin gwamnatin ta Bauchi, lura da yadda yunƙurin zai taimaka matuƙa wajen rage ɗimbin yaran da ke gararamba ba tare da zuwa makaranta ba a Arewacin na Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
-
Ɓanagrorin ilimi sun koka da matakin JAMB na durkusar da harshen Faransanci
24/10/2024 Duración: 10minSannu a hankali darussan nazarin harshen faransanci na kara karbuwa a manyan makarantun Nigeria, sai dai kuma, wani matakin da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB a Nigeria, ta aiwatar, na cire takardar shaidar share fagen shiga jami’a ta karatun harshen faransanci, daga cikin darussan da hukumar ta JAMB ke bayar da guraben karatunsu a manyan makarantu ya daga hankalin masu ruwa da tsaki.
-
Yadda wasu gwamnoni a Najeriya ke biris da yaran talakawa da suka tura karatu wasu kasashe
15/10/2024 Duración: 10minShirin na wannan rana ya duba yadda wasu gwamnonin a Najeriya ke daukar alhakin tura yaran talakawa wasu kasashe domin karatu amma kuma daga bisani sai gwamnatin ta yi biris da sha'aninsu.
-
Yadda jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI
08/10/2024 Duración: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba yadda wasu manyan jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin ƙasashen da suka ci gaba kan yadda za a inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI. Tuni kuma suka gabatar da wannan buƙata tasu a wajen taron da ƙungiyar bunkasa ilimi ta ƙasashen Turai kan shirya duk shekara, inda a wannan shekara Faransa ta karbi baƙuncin irin wannan taro da ya samu halartar jami'oi 6 da aka zabo daga Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.......
-
Yadda ake ƙara samun yawaitar masu karatun yaƙi da jahilci a Adamawa
01/10/2024 Duración: 09minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna ne akan yadda makarantun manya ko kuma na yaƙi da jahilci kamar yadda akan kira su, ke fuskantar ƙalubalen ɗauka ko ilimantar da ɗaliban da yawansu ke ƙaruwa a kullum, adadin da ya zarta na makarantun manyan da ake da su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara......
-
Hukumar JAMB ta shirya taro kan bai wa naƙasassu dama
24/09/2024 Duración: 10minShirin namu na wannan mako zai yi dubi ne kan yadda hukumar kula da harkar jarabawan shiga jami’o’i a Najeriya wato JAMB da hadin guiwan kungiyar zabiya na kasa ta shirya taron nahiyar Afrika na farko kan baiwa nakasassu ko masu larura ta musamman dangane da harkar ilimi kamar kowani dan adam. Taron an shirya shi ne dai la’akari da irin kalubalen da masu larura ta musamman ke fama da ita a kasashe masu tasowa kamar Najeriya,kama daga kyama,nuna musu banbanci da dai sauransu.
-
Fannin ilimi a Najeriya na fuskantar barazana sakamon matsin tattalin arziki
17/09/2024 Duración: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya yi duba ne a kan yadda matsin tattalin arziki da kuma tsare-tsaren gwamnati suka kassara fannin ilimi a tarayyar Najeriya. Daga ɓangaren mahukunta jami'o'in suna ganin tsare-tsaren da gwamnati ta bullo da su a fannin ilimi sune suka sanya a wannan lokaci ko da gyare-gyare a jami'o'in basa iya aiwatarwa. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara........
-
Har yanzu tsarin jagoranci da bada shawarwari na tasiri a makarantu?
27/08/2024 Duración: 09minShirin a wannan mako ya duba yadda tsarin jagoranci da bada shawarwari a makarantu, tsarin da ke taimakawa dalibai zabar irin fannin da suke son kwarewa akai, inda sun kai matakin jami'a da sauransu. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara
-
Tsarin ilimin Sakandire kyauta a Ghana ya ƙarfafa gwiwar dubban ɗalibai
20/08/2024 Duración: 09minShirin ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara a wannan makon ya mayar da hankali kan tsarin bayar da ilimin Sakandiren kyauta a Ghana, wanda ya taimaka matuka wajen ƙara yawan Ɗaliban da ke halarta karatu a wannan mataki. Duk da cewa shirin ya laƙume kuɗaɗe masu tarin yawa amma gwamnatin ƙasar ta Ghana ta ce ko shakka babu kwalliya ta biya kuɗin sabulu cikin shekaru 5 da fara tsarin.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shiri.
-
Yadda tsarin koyo da koyarwa a karni na 21 ke saukakawa wurin fahimtar karatu
30/07/2024 Duración: 09minA wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan tsarin dabarun koyo da koyarwa a ƙarni na 21 da ake kira da 21st Century Learning Skills a turance.Tsarin dabarun koyo da koyarwa na ƙarni na 21, an soma amfani da shi tun a shekarar 2001 domin zamanantar da tsarin yadda ake koyarwa ta hanyar samar da dabarun zamani da za su taimaka wa malamai wurin fahimtar da ɗalibai, sannan ɗalibai su ma su ji sauƙin fahimtar abin da ake koyar da su a aji. A wannan mako, mun dubi yadda tsarin yake aiki tare yadda ya sauƙaƙa wa malamai da ɗalibai wurin fahimtar karatu a wannan zamani musamman a ƙasashe masu tasowa irin Najeriya.Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
-
Karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana
23/07/2024 Duración: 09minShirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana. Hukumar kididdiga ta kasar GSS ta gano cewa kusan matasa miliyan biyu ne ba sa karatun Boko ko aikin yi ko kuma samun horon sana'o'in dogaro da kai.Ku danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadeer Haladu Kiyawa.
-
Yadda tsadar lantarki ke kassara harkokin karatun manyan makarantun Najeriya
16/07/2024 Duración: 10minA wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki ke gurgunta harkokin karatu a manyan makarantun Najeriya.Kamar yadda aka sani, harkokin gudanarwar yau da kullum na manyan makarantu ba za su taɓa yiwu wa yadda ya kamata ba, muddin babu ingantacciyar wutar lantarki. To sai dai, baya ga rashin tsayayyiyar wutar a kusan manyan makarantun Najeriya, wata matsalar kuma ita ce ta tsadar wutar a sakamakon ƙarin farashin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin ƙasar ta yi.Wannan dalili ne ya sanya ƙungiyar shugabannin jami’o’in Najeriya, ta yi kashedin cewa jami’o’in tarayyar ƙasar aƙalla 52 ka iya durƙushewa nan ba da jimawa ba, a sakamakon tsadar kuɗin wutar.Shugabannin Jami’o’in na Najeriya, sun yi wannan gargaɗi ne bayan wani sabon ƙari na kashi 300 da aka yi musu a kwanakin baya.Kuna iya latsa alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin...
-
Dalilan mummunar faduwar jarabawa da daliban jamhuriyar Nijar suka yi a bana
09/07/2024 Duración: 09minShirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda dalibai a jamhuriyar Nijar suka yi mummunar faduwa a sakamakon jarabawar karshe ta makarantar Sakandare. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadir Haladu kiyawa
-
Yadda ayyukan ƴan ta'adda suka kassara harkokin Ilimi a Arewacin Najeriya
02/07/2024 Duración: 09minA wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan yadda hare-haren ‘yan ta’adda suka kassara harkokin ilimi a arewacin Najeriya, shekara 10 kenan da 'yan ta'adda suka fara kai hari kan makarantu a Najeriya, lamarin da ya fara faruwa a shekarar 2014 a makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Chibok da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin kasar. Bincike ya nuna cewa, tun bayan harin na 2014, 'yan ta'adda sun ci gaba da kai makamancinsa a kimanin makarantu 17, waɗanda suka haɗa da makarantun Firamare da sakandare da ma manyan makarantun gaba da sakandare, inda suka yi garkuwa da dalibai da dama, an sako wasu bayan biyan kuɗin fansa, wasu kuwa suna rike a hannunsu har zuwa yanzu. Cikin shekaru goma da fara ƙaddamar da irin wannan ta'addanci kan makarantu da ɗalibai, masana sun bayyana shakku kan gwamnatin Najeriya tare da zarginta da nuna halin ko in kula kan ilimi tare da rayukan al'ummar kasar musamman ɗalibai. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...
-
Tasirin sabuwar hanyar koyarwa a duniya
25/06/2024 Duración: 09minA wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan sabuwar hanyar koyarwa, da kuma tasirin da ta ke da shi a harkar ilimi a faɗin duniya, wato Innovative Teaching Method a turance. Ita dai sabuwar hanyar koyarwa wato Innovative Teaching Method, hanya ce da ta sha bambam da hanyoyin koyarwa da aka saba gani a lokutan baya, domin ita ana koyar da ɗalibai ne bisa doron buƙatarsu ta koyo, ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani da kuma na’urori, batare da malami ya zama shi ne ruwa kuma shi ne langa ba.
-
Yadda jaddawalin karatun Najeriya ke haifar ga koma-baya a Fannin Ilimin Kasar
18/06/2024 Duración: 09minA wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne a kan yadda tsarin jaddawalin karatun Najeriya ke haifar da koma-baya a fannin ilimin kasar. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...
-
Ban-bancin da ke da shi wajen karatun Ilimin kimiyya da fasaha a kasashen Duniya
11/06/2024 Duración: 09minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne a kan tsarin ilimin kimiyya da fasaha tsantsa hadi da lissafi, wato STEM Education a turance. Mafi yawancin kasashen Duniya da suka ci gaba, na bawa wannan tsari na Ilimin Kimiyya da fasaha tsantsa hadi da Lissafi fifiko a makarantunsu, la’akhari da yadda kimiyya da fasaha a wannan zamani suka zama ginshinkin ci gaba a sararin wannan duniyar. Kuna iya latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......
-
Jami'ar Umaru Musa ta yaye sama da dalibai dubu goma a wannan shekarar
04/06/2024 Duración: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda ake ci gaba da samun ci gaba a bangaren daliban da ke zuwa makaranta a yankin Arewacin Najeriya. Jami'ar Umaru Musa 'Yar Adu'a da ke jihar Katsina ta samu nasarar yaye sama da dalibai dubu 10 a wannan shekarar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin ta re da Abdulkadir Haladu Kiyawa........
-
Yadda Jami'o'in Najeriya suka fara mayar da hankali kan karatun koyon sana'a
21/05/2024 Duración: 09minShirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda aka fara mayar dahankali a kan karatun koyon sana'a a Kwalejoji da Jami'o'i a Najeriya.Kuna iya Latsa alamar sauti domin sauraron shirin...