Sinopsis
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.
Episodios
-
Yadda Dalibai ke bada gudunmawa wajen sarrafa sinadaran da basa gurbata muhalli
14/05/2024 Duración: 10minShirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya duba yadda Dalibai a kasashen da suka ci gaba ke bayar da gudunmawa wajen sarrafa sinadarin "Hydrogene" da baya gurbata muhalli sosai, ta fuska kere-kere da nufin inganta iskar da ake shaka, bisa tallafin gwamnatocin kasashensu.
-
Yadda matasa ke dukufa wajen amfani da Internet don dogaro da kai
07/05/2024 Duración: 10minShirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako zai duba yadda matasa suka dukufa wajen amfani da yanar gizo don dogaro da kai. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
-
Karuwar masu mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya, na barazana ga karewar kwararru
26/03/2024 Duración: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya duba yadda mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya ke barzana ga karewar kwararru a fannoni da dama. Ana fargabar idan har wannan dabi'a ta ci gaba a haka, tabbas za'a rasa kwararru musamman a fannin lafiya, kimiyya da sauransu.Danna Alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
-
An samar da cibiyar sadarwa a jahar Bauchi don saukakawa dalibai wajen bincike
19/03/2024 Duración: 09minShirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda wasu kungiyoyi karkashin cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma wato CITAD suka samar da wata katafariyar cibiyar sadarwa da aka yiwa lakabi da HELLO HOPE a jahar Bauchi. Shirin ya kasance wani bangare na yunkurin saukakawa mazauna karkara hanyoyin samun sadarwa ta internet musamman wuraren da babu irin wannan ci gaba ko kuma wuraren da suke da shi amma bashi da karfi, wanda jama’are ke cikin wannan rukuni. Kungiyoyin da sun sha alwashin samar da irin wannan cibiyar sadarwa guda 20 a shiyoyin Najeriya shida zuwa karshen wannan shekara domin samar da internet a yankunan karkara.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........