Bakonmu A Yau

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

  • Farfesa Tukur Abdulkadir kan ziyarar da Blinken a yankin Gabas ta Tsakiya

    21/03/2024 Duración: 03min

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya sake komawa a Yankin Gabas ta Tsakiya a ci gaba da kokarin da kasashen duniya ke yi don samar da tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas. Daga farkon wannan rikici wanda ya barke a ranar 7 ga watan Oktoban bara zuwa yanzu, sau da dama Amurka na cewa tana yunkuri domin samar da tsagaita wuta a wannan yaki da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu 35 da kuma raba sama da milyan biyu da gidajensu. Farfesa Tukur Abdulkadir malami a jami’ar jimi’ar jihar Kaduna, na ganin cewa, da dagaske Amurka ke yi, da tuni an kawo karshen wannan yaki.Ku latsa alamar sauti don jin zantawarsa da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.......

  • Nastura Ashir Sharif kan kalaman da ke kokarin kawo rabuwar kai a Najeriya

    20/03/2024 Duración: 03min

    Gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya CNG, ta yi zargin cewa a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsalar tsadar rayuwa, wasu ‘yan siyasa musamman a cikin majalisun dokokin kasar na furta kalamai da kuma manufofi da ke neman raba kan al’ummar kasar. Kawancen CNG ya bayar da misali da abubuwan da suka faru a zauren Majalisar Dattawan kasar bayan da Sen Abdul Ningi ya yi zargin yin cushe a cikin kasafin kudin kasar na wannan shekara, lamarin da ya kai ga dakatar da shi na tsawon watanni uku. Muhammad Sani Abubakar ya zanta da shugaban majalisar amintattu na kungiyar CNG Nastura Ashir Sharif a game da wannan batu.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar ta su.....

  • Umar Kabir Dan Anini kan katsewar sadarwar da aka samu a wasu kasashen Afrika

    19/03/2024 Duración: 03min

    A makon da ya gabata ne aka samu katsewar sadarwar intanet a wasu kasashen Tsakiya da Yammacin Africa, sakamakon yankewar wasu wayoyin karkashin ruwa na sadarwar kamar yadda masana suka bayyana, lamarin da ya haifar da gagarumar koma baya a fannin tattalin arziki da harkokin yau da kullum a kasashen da matsalar ta fi shafa. Akan hakan ne Isma'il Karatu Abdullahi ya zanta da Umar Kabir Dan Anini, kwararre a fannin fasahar sadawa a Najeriya, dangane da tasirin yankewar sadawar da aka samu musamman a fannin tattalin arziki a kasashen da abin ya shafa.Ku latsa alamar sauti don saurarron tattaunawarsu......

  • Farfesa Dicko Abdourahmane kan kawo karshen alakar tsaro tsakanin Nijar da Amurka

    18/03/2024 Duración: 03min

    Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka, tare da zargin cewa dakarun Amurka wadanda adadinsu ya zarta dubu daya na zaune a kasar ne ba a kan ka’ida ba. Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da wata babbar tawagar Amurka ta kamma ziyarar da ta kai Nijar ta tsawon kwanaki uku. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Farfesa Dicko Abdourahmane, masani tsaro kuma malami a jami’ar Damagaram Zinder, wanda da farko ya fara yin bayani a game da dalilan da suka sa mahukuntan Nijar suka dauki wannan mataki.Ku latsa alamar sauti don jin zantawarsu.......

  • Alhaji Sirajo Jankado Sarkin Hausawa Turai kan batun bakin haure

    14/03/2024 Duración: 03min

    Daya daga cikin matsalolin da suka addabi nahiyar Turai a wannan lokaci, shine batun bakin haure, ganin yadda matasa daga nahiyar Afirka ke tafiya mai hadari cikin kwale kwale da zummar zuwa nahiyar, abinda ke kai ga rasa rayuka da dama. Dangane da wannan matsala da kuma matakan da magabata ke dauka wajen fadakar da al'umma illar irin wannan tafiya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sarkin Hausawa Turai Alhaji Sirajo Jankado a fadarsa da ke kasar Faransa, kuma ga yadda zantawar su ta gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu......

  • Dr Aliyu Sabi kan matakin Najeriya na sanya dokar ta baci a bangaren noma

    13/03/2024 Duración: 03min

    Nigeria ta kaddamar da dokar ta baci a game da harkar noma, inda ta fidda tsare-tsare da dama don shawo kan matsalar karancin abinci da kasar ke fama da ita a cikin gaggawa, wannan kuwa ta la’akari da waharhallun da jama’a ke ciki.  A ci gaba da gabatar da rahotanni da kuma hirarraki dangane da matsalolin da bangaren noma ke fuskanta a Najeriya, a yau za mu ji tattaunawa da karamin minista a ma’aikatar noma ta kasar Sanata, Dr. Aliyu Sabi Abdullahi.Ga kuma abun da yake cewa.Ku danna alamar saurare don jin cikakken rahoton

  • Yahuza Getso kan fargabar gwamnatin Najeriya na kai hari karin wasu makarantu

    12/03/2024 Duración: 03min

    Yayin da ake ciki gaba da samun karuwar satar dalibai a Najeriya, Gwamnatin kasar ta bayyana fargabarta tare da yin gargadin cewa za’a iya kaiwa wasu makarantu a jihohin kasar 14 har da babban birnin tarayya Abuja.Shin hakan ya nuna gazawar gwamnatin kasa ta fannin tsaro kenan? Abdulkadir Haladu Kiyawa, ya tattauna da Dakta Yahuza Ahmad Getso masanin tsaro a Najeriyar.

  • Sheikh Sani Yahaya Jingir kan fa'idar azumin watan Ramadan

    11/03/2024 Duración: 02min

    A yayin da alummar musulmi daga kasashe da dama na duniya suka fara Azumin watan Ramadan, daya daga cikin manyan malaman addninin musulunci a Nijeriya, Sheikh Muhamad Sani Yahaya Jingir, ya yi karin haske akan irin fa'idar dake tattare da Azumin watan Ramadan ga abun da yake cewa a zantawarsu da wakilinmu na Jos Tasiu zakari.

  • Saudatu Abubakar kan bikin ranar mata ta duniya

    08/03/2024 Duración: 03min

    Ranar 8 ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don bikin ranar mata da ke da aniyar lalubo matsalolin da mata ke fuskanta da kuma duba hanyoyin warware su. Bikin ranar na bana dai ya zo ne a dai-dai lokacin da mata ke fuskantar matsin rayuwa sanadin tashe-tashen hankula da kuma tsananin talauci.Kan bikin wannan rana, Michael Kuduson ya tattauna da Saudatu Abubakar Kabir, shugabar mujallar Muryar Matan Afirka.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Tattaunawa da Dakta Nazifi Wada Salisu Maigatari kan dambarwar Hisba a Kano

    06/03/2024 Duración: 03min

    ‘Yan Najeriya a ciki da wajen kasar na ci gaba da tattaunawa akan yadda masu shiga tsakani suka sansanta tsakanin gwamnatin Kano da babban kwamandan hukumar Hisba Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa, biyo bayan sabanin da ya kai ga sanarwar yin Murabus da shugaban hukumar yayi. Wannan al’amari da kuma dalilan da suka haifar da aukuwarsa na cigaba da daukar hankalin jama’a da ke bayyana ra’ayoyinsu akai.Kan haka ne Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Nazifi Wada Salisu Maigatari, Malami a Jami’ar Tarayya da ke garin Dutse a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar......

  • Umar Alangawari kan kai wa motocin dakon kayan abinci da rumbuna hari

    05/03/2024 Duración: 03min

    Batun kai hari tare da daka wawa kan rumbunan ajiyar kayayyakin abinci na hukumomi a wasu yankunan Najeriya na neman zama ruwan dare, la’akari da yadda a ‘yan kwanakin nan hakan ta rika faruwa, yayin da kuma a wasu lokutan aka rika tare motocin dakon abincin tare da afka musu, lamarin da ake alakantawa da tsananin tsadar rayuwa da yunwar da ke addabar dimbin mutane a Najeriya. To ko yaya direbobin manyan motocin dakon abinci suka ji da halin da aka shiga, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Umar Garba Alangawari daya daga cikin masu motocin dakon kaya a Najeriyar.

  • Muhammadu Magaji: Kan yadda Najeriya za ta inganta harkar noma

    01/03/2024 Duración: 03min

    Masana harkar noma da samar da abinci sun bayyana cewar Najeriya na da duk abinda take bukata wajen ciyar da kan ta muddin ta inganta harkar noman kasar, amma kuma sakaci daga hukumomi da matsalar tsaro na ci gaba da yiwa kasar tarnaki. Wasu na danganta matsalolin da ake fuskanta daga sakacin gwamnati, yayin da wasu ke zargin jama’ar kasar da kauracewa rungumar aikin noman.Dangane da wannan matsala na gazawar kasar wajen ciyar da kan ta, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sakataren tsare tsare na kungiyar manoman Najeriya, Alhaji Muhammadu Magaji.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Mu'azu Magaji: Kan dambarwar Hisbah da gwamnatin Kano

    01/03/2024 Duración: 03min

    Yau al’ummar Jihar Kano dake Najeriya sun tashi da labarin murabus din da shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi daga mukamin sa, sakamakon abinda ya kira sanyaya masa gwuiwar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, wajen sukar yadda suke gudanar da aikin su. Wannan murabus din ta haifar da mahawara mai zafi a ciki da wajen jihar Kano, tare da hudubobi a Masallatan Juma’a dangane da muhimmancin hukumar da kuma rawar da take takawa.Tsohon kwamishinan ayyuka a Jihar kano, Hon Muaz Magaji, ya ziyarci ofishin RFI dake Lagos, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi a kan dambarwar.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Alhaji Mukhtar Hussain kan maido da tsarin bai wa ‘yan canji dala da CBN yayi

    28/02/2024 Duración: 03min

    Babban Bankin Najeriya ya maido da tsarin bai wa ‘yan canji dala, a wani mataki na farfado da darajar Naira wadda ta fadi warwas a kasuwar hada-hadar kudade. CBN ya ce, zai rika sayar wa masu lasisi dala dubu 20 a kan farashin Naira dubu 1 da 301, yayin da ya shinfida musu wasu ka’idoji da suka hada da cin ribar da ba ta wuce kashi 1 na farashin da ya sayar musu da dalar ba. Ko ya masana tattalin arziki ke kallon wannan mataki? Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Alhaji Mukhtar Hussain.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar tasu.......

  • Comrade Nasir Kabir kan zanga-zangar lumanar kungiyar kwadago ta Najeriya

    27/02/2024 Duración: 03min

    Yau kungiyoyin kwadago a Najeriya ke gudanar da zanga-zangar lumana a kan tsadar rayuwa, sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar tayi, wanda ya haifar da mummunar hauhawan farashin kayan masarufi. Kungiyar NLC ta kira zanga-zangar a biranen kasar wajen ganin gwamnati ta saurari korafe-korafen jama'a dangane da halin kuncin da suka samu kan su. Dangane da wannan zanga-zangar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da sakataren tsare-tsare na kungiyuar NLC Comrade Nasir Kabir.Ku latsa alamar sauti don sauraron  zantawar ta su.......

  • Amb Ibrahim Kazaure kan janye takunkumin ECOWAS ga kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso

    26/02/2024 Duración: 03min

    Kungiyar ECOWAS ta sanar da janye takunkumin karya tattalin arzikin da ta sanyawa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, yayin da ta bukaci sojojin da suka yi juyin mulki a wadannan kasashe da su dawo teburin tattaunawa domin samo hanyar mayar da mulkin dimukiradiya a cikin su. Shugabannin ECOWAS sun ce an cire takunkumin ne saboda dalilan jinkai, kuma matakin ya kawo karshen hana zirga zirgar jiragen sama da bude asusun ajiyar wadannan kasashe guda 3. Dangane da tasirin wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ibrahim Kazaure, masanin harkar diflomasiya.Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawar su ta gudana.....

  • Abdou Jibo kan takunkumin da ECOWAS ta sanyawa Jamhuriyar Nijar

    23/02/2024 Duración: 03min

    Kungiyar ‘Yan Nijar mazauna Cote d’Ivoire ta bukaci a cirewa Nijar takunkumai da aka kakaba mata sakamkon juyin mulki da sojoji suka yi, saboda halin kunci da hakan ya jefa su ciki. Shugaban kungiyar ta Ho consei de Nijar a Cote d’Ivoire Alhaji Abdou Jibo ya yi wannan kira, yayin zantawa ta musamman da sashin hausa na RFI a Abidjan.Amma ya fara yi wa Ahmad Abba bayani kan zamantakewarsu a kasar da ke mamba a ECOWAS.Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar

  • Alhaji Umaru Garkuwa kan umarnin kama masu hada-hadar kudaden kasashen ketare

    21/02/2024 Duración: 03min

    Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin kama masu hada-hadar kudaden kasashen ketare saboda zargin da ake musu na karyewar darajar naira da kuma boye kudaden ketare da mabukata ke nema ruwa a jallo. Tuni dai aka kama wasu daga cikin 'yan kasuwar a Abuja, yayin da darajar nairar ta dada faduwa, inda ake sayar da dalar Amurka guda a kan naira dubu 1,800. Dangane da wannan takun saka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da daya daga cikin 'yan kasuwar chanji na Abuja, Alhaji Umaru Garkuwa.Sai ku danna alamar sauti don sauraron tattaunawarsu....... 

  • Malam Isa Sanusi kan warware rikicin ECOWAS da Nijar da Mali da Burkina Faso

    20/02/2024 Duración: 03min

    Kungiyar ECOWAS na ci gaba da lalubo hanyar warware rikicin da ke tsakanin ta da kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina wadanda sojoji suka yi juyin mulki. Tuni kungiyar ta sanya musu takunkumin karya tattalin arziki, yayin da su kuma kasashen suka ce sun fice daga cikinta. A karshen wannan makon ne ake saran ECOWAS ta gudanar da taro na musamman domin nazari a kan rahotannin da take karba dangane da wadannan kasashe. Dangane da wannan takun saka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da daraktan Kungiyar Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sanusi.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu........  

  • Shu'aibu Idris Mikati kan karyewar darajar kudin Najeriya

    19/02/2024 Duración: 03min

    Farashin dala na ci gaba da hawa a kasuwar musayar kudade a najeriya, inda a ranar Litinin farashin ya tasama naira 1,712 kan dala guda, abin da masana tattalin arzikin kasar ke zargin CBN na da hannu a wannan matsalar. Wannan lamarin na bayyana yadda darajar kudin kasar ke ci gaba da samun koma baya, abin da masana ke ganin shine mafi muni da aka taba samu a tarihin kasar.Kan wannan matsala ne, Bashir Ibrahim Idris, ya tattauna da Alhaji Shu'aibu Idris Mikati, masanin tattalin arziki a Najeriya.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

página 1 de 2