Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Babu sojan da zai yi ritaya a wannan shekarar a Jamhuriyar Nijar
06/05/2025 Duración: 03minGwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta bai wa hafsan sojojin ƙasar umarnin cewar babu wanda zai tafi ritaya a cikin wannan shekarar, sakamakon wasu matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta. Dangane da wannan umarni, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Sani Yahya Janjuna, mai sharhi akan lamuran yau da kullum, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai.
-
Tattaunawa da Hon Samaila Muhammed kan barazanar Meta na ficewa daga Najeriya
05/05/2025 Duración: 03minKatafaren kamfanin sadarwar Meta da ya mallaki Facebook da WhatsApp ya yi barazamar ficewa daga Najeriya, saboda cin tararsa da hukumomin ƙasar suka yi na Dala miliyan 290, sakamako karya ƙa’idodin aikinsa. Najeriya ta samu kamfanin ne da laifin talla ba bisa ƙa’ida ba, da kuma rashin alkince bayanan asiri na jama’ar dake hulɗa da shi.Dangane da wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon Samaila Muhammed, masanin tallalin arziki da kuma sadarwa, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar
-
Dr. Harbau: Yadda ma'aikata za su nema wa kansu mafita
01/05/2025 Duración: 03minYau ɗaya ga watan Mayu take ranar Ma’aikata ta Duniya, ranar da ake duba gudummawa da sadaukarwar ma’aikata ga al’umma. A kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Dokta Aminu Idris Harbau, masanin tattalin arziki a jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke jihar Kano a Najeriya, wanda ya duba yadda wannan rana ta riski ma’aikata, tare da shawartar su a kan nema wa kansu mafita a yanayi da albashi ba zai wadata ba wajen tafiyar da rayuwa mai inganci.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakakkiyar hirarsu