Sinopsis
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episodios
-
Lafiya Jari ce: Illar da hayaƙin girki ke yiwa lafiyar idon Mata
11/11/2024 Duración: 10minA wannan makon shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan wani gargaɗin masana game da illar hayaƙi ga lafiyar jama’a a wani yanayi da masanan ke ganin mazauna garuruwa irin Kano da Sokoto da Kwara baya ga kaso mai yawa na jihohin arewacin Najeriya na cikin haɗarin kamuwa da cutukan masu alaƙa da numfashi sakamakon yadda suka dogara da itace ko kuma gawayi wajen yin girki. A ɓangare guda wasu ƙwararrun na ganin matan da suka shafe lokaci suna girki da itace ka iya fuskantar matsalar ido, tambayar a nan ita ce ko matan na da masaniya kan illar hayakin girki ga lafiyar idonsu? Ku biyo mu a cikin shirin don sauraren mahangar masana da kuma yadda Mata ke kallon illar ta hayaƙin girki ga lafiyarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....
-
Yadda cutar kwalara ta addabi wasu jihohin arewacin Najeriya
04/11/2024 Duración: 09minShirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar Kwalara ko Amai da Gudawa da ta afkawa wasu jihohin Najeriya, inda ta haifar da asarar ɗumbin rayuwa tun bayan ɓullarta a farkon wannan shekara ta 2024
-
Ƙuncin rayuwa na jefa ɗimbin ƴan Najeriya cikin tsananin damuwa - Rahoto
28/10/2024 Duración: 09minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan matsalar damuwa mai dankwafarwa ko tsananin damuwa da ake kira Depression, cutar da ake ganin ta’azzararta a baya-bayan nan tsakanin ƙasashe masu tasowa musamman waɗanda ke fama da matsi ko kuma ƙuncin rayuwa. Wasu bayanan ƙwararru yayin bikin ranar lafiyar ƙwaƙwalwa da ya gudana a farkon watan nan, ya nuna yadda matsi da ƙunchin rayuwa ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya a tsananin damuwar ko kuma damuwa mai dankwafarwa, matsalar da likitoci suka yi gargaɗin cewa ka iya kaiwa ga taɓin ƙwaƙwalwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........
-
Yadda mutane ke kauracewa yin gwaje-gwajen lafiya na wajibi
21/10/2024 Duración: 09minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon yayi duba ne kan ƙalubalen da fannin lafiya ke fuskanta na yadda ake gani a halin yanzu jama’a ke tsoro ko kuma kaucewa gwaje-gwajen lafiya ciki kuwa da har da wajibi da suka ƙunshi hawajini da nau’in jini ko kuma rukuninsa duk kuwa da muhimmancin hakan ga lafiyarsu. A baya-bayan nan bincike ya gano yadda jama’a kan kaucewa yin gwaje-gwaje kama daga na wajibi ko kuma a lokacin kamuwa da cutuka, walau ko saboda tsoron gano wasu nau’in cutuka da ke tare da su ko kuma wani dalili na daban.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......
-
Illar shan magani ba tare da shawarar masana kiwon lafiya ba
14/10/2024 Duración: 09minShirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne game da matsalar shaye-shayen magunguna ba bisa ka'ida ko kuma shawarwarin masana kiwon kiwon lafiya ba, wadda hakan ke haifar da matsaloli da dama a jikin dan'adam. 14/10/2024
-
Illar da hayaƙin taba sigari ke da shi ga lafiyar al'umma
07/10/2024 Duración: 10minShirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne game da matsalar zuƙar taba sigari a cikin al'umma saɓanin wasu keɓantattun wurare da doka ta tanada. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce a duk shekara sama da mutane miliyan 8 ne ke mutuwa sanadiyar shakar hayakin taba sigari kuma daga cikin wancan adadi, akwai sama da yara dubu 65 waɗanda lamarin ke shafa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
-
Yadda ake samun ƙaruwar masu fama da cutar amasonin jini
30/09/2024 Duración: 09minShirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda ake ganin ƙaruwar masu fama da cutar amasonin jini, ko Sickler ko kuma Emasi, batun da ke da alaƙa ta kai tsaye da auratayyar da ake yi tsakanin masu nau’ikan jinin da masana ke gargaɗi kan illar da hakan ke da shi ga ƴaƴan da za su haifa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
-
Tsanantar cutar ƙoda da abubuwan da ke haddasa ta a tsakanin al'umma
23/09/2024 Duración: 09minA wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan abubuwan da ke haddasa cutar koda, la'akari da yadda cutar ke tsananta a wannan lokaci musamman a kasashe irin Najeriya, sabanin a lokutan baya da ba kasafai ake ganinta ba, baya ga karancin wuraren wankin kodar da ake fama dasu wato dialysis centers a turance. Wani bincike na baya-bayan nan na nuni da cewa cutar koda ita ce ta 10 cikin cututtukan da ke kan gaba wajen haddasa mace-mace a fadin duniya, inda binciken ya nuna cewa kuma tana shafar kusan kashi 10 na al'ummar duniya, wanda a halin yanzu sama da mutane miliyan 850 ke fama da ita.
-
Abubuwan da ke haddasa tsinkewar laka ga ɗan Adam
20/09/2024 Duración: 09minShirin lafiya jarice na wannan mako ya mayar da hankali ne kan cutar katsewar laka wacce ke iya afkuwa a sanadiyar hadarin mota ko makamantansu da rikice-rikice ko fadowa daga wurare masu tudu da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
-
Yawaitar masu fama da lallurar laka a sassan Najeriya
16/09/2024 Duración: 09minA wannan mako shirin zai mayar da hankali game da cuta ko kuma ‘‘lalurar katsewar Laka’’ wato Spinal cord Injury, lalurar da a baya-bayan nan alƙaluma ke nuna yawaitar masu fama da ita a sassan Najeriya, walau sakamakon haɗarin mota ko rikici dama sauran dalilai. Yayin bikin ranar wayar da kai game da lalurar ta Laka da ke gudana a kowanne wata na Satumba, da a wannan karon aka yiwa take da ‘‘ Kawar da tarzoma a matsayin hanyar kawar da laka’’ masana sun ce baya ga haɗurran mota hanyoyi da dama na haddasa wannan lalura ta laka.
-
Yadda cutar borin gishiri ke addabar mata masu juna biyu a Jamhuriyar Nijar
09/09/2024 Duración: 10minA wannan makon shirin zai mayar da hankali kan cutar borin gishiri ko kuma kumburin da mata ke fama da ita yayin da suke da dauke da juna biyu, wacce kuma a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka. Wannan cuta a Jamhuriyar Nijar na daga cikin wacce ke ciwa hukumomi tuwo a kwarya ganin yadda mata sama da dari biyar da 30 cikin kowace mace dubu daya ne kamuwa da wannan cuta, kuma sama da 50 ke rasa ransu a sanadiyarta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
-
Ƙaruwar ƙananan yara da ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki
02/09/2024 Duración: 10minA wannan makon shirin zai mayar da hankali kan ƙaruwar ƙananan yaran da ke fama da cutar yunwa ko kuma Tamowa a yankunan da ke fama da ƙarancin abinci, cikinsu kuwa har da Nijar, ƙasar da alƙaluman 2021 ke cewa akwai ƙananan yara ƴan ƙasa da shekaru 5 akalla miliyan 1 da dubu 800 da ke fama da rashin abinci mai gina jiki. A baya-bayan nan anga ƙaruwar yaran da ke fama da cutar Tamowa ko da ya ke har yanzu akwai ƙaranci sani game da cutar, kan hakan mu ka fara da tuntuɓar Dr Fayuz Mu’azu likitan mai kula da ƙananan yara masu fama da cutar Tamowa a jihar Diffa, ya kuma yi mana bayani kan cutar da dalilan da ke haddasata.
-
Hatsarin da ke cikin amfani da maganin ƙwari wajen adana kayan abinci
22/07/2024 Duración: 09minShirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon zai mayar da hankalli ne a kan gargaɗin da hukumar kiyaye ingancin abinci da magunguna a Najeriya, wato NAFDAC ta yi a kan hatsarin da ke tattare da amfani da maganin kashe ƙwari na Sniper a wajen adana kayan abinci domin kare su daga ƙwari. NAFDACdai ta jaddada haramcin da ta yi a kan amfani da wannan magani da ma sshigowa da shi Najeriya, bayan da ce bincikenta ya tabbatar da cewa maganin yana haddasa cutuka da suka haɗa da cancer.
-
Tasirin sabbin abinci da aka ƙirƙira wato Synthetic Foods ga lafiyar jama'a
15/07/2024 Duración: 09minShirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna ne kan tasarin nau'ukan abinci da akan ƙirkira a ɗakunan bincike wadanda ake kira Synthetic foods a turance, domin nazari kan illolinsu ko kuma akasi ga lafiyar jama'a, duba da yadda nau'ukan abinci da nomansu akayi ba ko kiwo ke samun ƙarbuwa a wasu kasashen duniya.
-
Yadda cutar kansar bakin mahaifa ke hallaka mata a tarayyar Najeriya
01/07/2024 Duración: 09minShirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi duba ne kan yadda kansar bakin mahaifa ke hallaka Mata, musamman ƴan tsakanin shekaru 15 zuwa 44, a Najeriya. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron shirin...
-
Yadda mata ke rungumar tiyatar gyaran jinki duk da gargadin da likitoci ke yi
24/06/2024 Duración: 09minShirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya duba kan yadda mata ke yin tiyatar gyaran jiki ko sauya sura wato Cosmetics Surgery, wacce a yanzu mata da dama suka runguma, duk kuwa da yadda likitocin ke ganin hakan na da illa ga lafiyarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......
-
Tsarin kiwon lafiya da mahukunta ke dauka a Saudiyya
10/06/2024 Duración: 10minShirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya duba yanayin lafiyar mahajjata, a dai-dai lokacin da al'ummar Musulmai ke gudanar da ibadar hajji a Saudiyya. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu
-
Har yanzu 'yan Najeriya da dama basa cin gajiyar shirin Inshorar lafiya -Bincike
03/06/2024 Duración: 09minShirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan yadda har yanzu wasu daga cikin al’ummar Najeriya basa amfani da tsarin inshorar lafiya. A shekarar 2022 ne gwamnatin kasar ta sake dawo da dokar inshorar lafiya da aka samar tun 1999, a wani yunƙuri na sauƙaƙawa Jama’a samun kulawar lafiya cikin rahusa, lura da yadda kaso mai yawa na al’ummar ƙasar ke rasa kudaden iya kai kansu ga likitoci ko da suna cikin matsananciyar cuta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......
-
Yara 'yan kasa da shekaru biyar na gaza samun alluran rigakafin da ta dace
27/05/2024 Duración: 09minShirin na wannan mako ya duba yadda kananan yara musamman a Najeriya da sauran kasashe masu tasowa ke gaza karbar alluran rigakafin da ya kamata su samu kafin cika shekaru biyar da haihuwa.
-
Halin da ake ciki a yaki da cutar yunwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar
20/05/2024 Duración: 09minA wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya yi duba ne a kan halin da ake ciki a yaki da cutar Tamuwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar.