Sinopsis
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Episodios
-
Matakin da Hukumar CAF ta ɗauka kan Ghana ya bar baya da ƙura
30/09/2024 Duración: 09minA dai-dai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiyen wasannin sharen fagen samun gurbi a gasar lashe kofin Afrika, Hukumar Kula Ƙwallon kafar Afrika CAF ta ce filayen wasan ƙasar Ghana ba su da ingancin da ya kamata a ce an gudanar da manyan wasanni na kasa da kasa a cikin, matakin da ke kara nuna gazawar ƙasar. Ita dai hukumar CAF ta ce ba komai ya sanyata daukar wannan mataki ba, face yadda ta ce aƙwai rashin wadatatciyar ciyawa da rashin magudanun ruwa da dai sauransu a filin wasa na Baba Yara da ke birnin Kumasi, haka ta ce abin ya ke a sauran filayen wasanni irin na Cape Coast da kuma na Accra.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
An shiga mako na uku a gasar firmiyar Najeriya
23/09/2024 Duración: 09minShirin a wannan lokaci zai leka gasar Firimirar Najeriya wato NPFL Wanda aka shiga mako na uku da somawa.Gasar Firimiyar Najeriya na daga cikin manyan gasannin Lik-lik da ake ji da su a nahiyar Afrika, musamman idan akayi la’akari da yadda ƙungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa ke taka rawar gani a gasar zakarun Ƙungiyoyin Afrika.
-
Koma bayan da harkokin wasanni ke fuskanta a Najeriya
16/09/2024 Duración: 10minShirin a wannan makon zayyi duba ne kan koma bayan da harkar wasannin ke fuskanta a Najeriya.Najeriya daya ce daga cikin kasashen da suka yi suna a fagen wasanni a duniya, inda ake ganinta a sahun gaba wajen wakiltar nahiyar Afrika.To sai dai a baya-bayan nan kasar na fuskantar koma baya a bangare, musamman idan aka yi la’akari da rashin katabus din da ta yi a lokacin gasar Olympics da aka gudanar a birnin Paris.
-
Yadda aka kammala gasar Paralympics da birnin Paris ya karbi bakunci
09/09/2024 Duración: 09minShirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi duba ne kan yadda aka kammala gasar gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta nakasassu wato Paralympics da birnin Paris ya karbi bakunci, bayan kwashe tsawon kwanaki 11 ƴan wasa dubu 4 da dari 4 su na fafatawa a wasanni 22 da aka lashe lambobin 549. Kasar China ce dai ta jagoranci teburin lashe lambobin yabo na wannan gasa, bayan da ta lashe lambar zinari 94 da azurfa 76 sai kuma tagulla 50, a jumlace tana da lambobin yabo 220. Ku latsa alamar Sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......