Sinopsis
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episodios
-
Yadda Najeriya ke fuskantar tashin farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru 30
24/07/2024 Duración: 10minA wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da hukumar ƙididigar ta Najeriya ta fitar cewa an sake samun hauhawan farashin kayayyaki wanda ƙasar ba ta taɓa gani ba cikin shekaru 30, daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ke faɗi tashin kawowa al’umma sauƙi kan tsananin rayuwa da suke ciki, tare da amincewa da Naira dubu 70 a amatsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata. Shin ko hakan zai kawo sauƙi kan halin da ake ciki a ƙasar? Kuna iya latsa alamar sauti don jin amsar wannan tambaya tare da masana ta cikin shirin...
-
Gwamnatin Najeriya za ta yi odan abinci daga waje saboda tsadar rayuwa a ƙasar
17/07/2024 Duración: 10minShirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan sabon matakin gwamnatin Najeriya na sahale shigo da muhimman kayan abinci kamar su shinkafa da wake da alkama da masara ba tare da biyan ƙudin fito ba har tsawon watanni 5, domin rage tasirin tsaɗar kayan abinci da ƴan ƙasar ke fama da shi tun bayan ɗarewar shugaba Bola Ahmed Tinubu mulki a bara. A wani taron manema labarai da ya kira wannan Litinin, ministan noma da samar da abinci na Najeriya, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana sabon matakin, inda ya ce shugaba Tinubu ya amince da janye ƙudin fito da kuma haraji kan muhimman kayan abincin ne har na tsawon kwanaki 150, domin wadatuwar kayan a Najeriya.Sanarwar ta ce baya ga janye ƙuɗin fito ga ƴan kasuwa masu bukatar shigo da kayan abinci, ita kanta gwamnatin tarayya za ta shigo da alkama da Masara kimanin tan dubu 250 kowanensu, domin bai wa kamfanoni jihohi da ke sarrafa su.
-
Yadda gwamnatin Nijar ta saukaka farashin shinkafa ga al'ummar kasar
03/07/2024 Duración: 09minShirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali kan yadda gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta fara saidawa talaka shinkafa a farshi mai rahusa, domin saukakawa ƴan kasar radadin matsin tattalin da suke ciki sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi. A ranar 26 ga watan Yunin da ya gabata gwamnatin Nijar ta hannun ma’aikatar kasuwanci ta kaddamar da wannan shirin, inda ake sayar da buhu mai nauyin kilo 23 kan jaka 13 da rabi maimakon jika 17 zuwa jika 19 da ake sayar da shi a a wasu wurare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......