Tambaya Da Amsa

Informações:

Sinopsis

Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.

Episodios

  • Bayani a kan ayyunkan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO

    15/06/2024 Duración: 19min

    Shirin 'Tambaya Da Amsa' wanda ya ke zuwa duk mako a wannan tasha zai amsa tambayar da ke neman bayanni a kan ayyukan Hukumar Lafiya ta Duniya,,musamma inda take samun kuɗaɗen gudanar da ayyukanta da kuma yadda taa ke ɗaukar ma'ikata.

  • Amsar tambaya game da muhimmancin taken ƙasa wato National Anthem

    08/06/2024 Duración: 18min

    Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru sani kamar kowanne mako ya na gayyato ƙwararru ne don amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana.  A wannan mako, shirin ya amsa tambaya game da tasirin taken ƙasa da ake kira National Anthem a Turance.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..

  • Tarihin tsohon shugaban Iran Ebrahim Raisi da bayani akan ma'askin dare

    01/06/2024 Duración: 20min

    Shirin tamabaya da amsa na wannan mako zai kawo muku tarihin shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar 19 ga watan Mayun shekarar 2024, tare da bayani akan ma'askin dare kamar yadda aka aiko mana da tambayoyi akansu, sai a kasance tare da mu a cikin shirin.

  • Bayani kan kotun ICC da kuma sammacin kamo firaministan Isra'ila da shugabannin Hamas

    25/05/2024 Duración: 20min

    Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aiko mana ciki harda amsar tambaya da ke neman bayani a game da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC da batun sammacin  kama firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da wasu shugabannin ƙungiyar Hamas. Ku latsa alamar sautin donjin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.........

  • Bayani a kan kamanceceniyar mulkin gurguzu da kama-karya

    04/05/2024 Duración: 20min

    Shirin, wanda  ke zuwa muku duk mako a lokacin irin wannan, yana kawo muku amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da wasu daga cikin masu bibiyanmu suka aiko mana ne, kuma a yau, za ku ji amsar tambayar da ke neman ƙarin bayani a kan salon mulkin gurguzu, da kuma ko da gaske yana  da kamanceceniya da mulkin kama-karya kamar yadda masu kushe shi ke fadi. Sai a kasance tare da  mu.

  • Hukumar samar da wutar lantarki ta yi bayani game da kudin wuta da jama'a za su biya a Najeriya

    13/04/2024 Duración: 20min

    ‘Tambaya Da Amsa’ shiri ne da ke kawo amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana. Bayan janye tallafin lantarki a Najeriya, hukumar samar da wutar ta yi bayani  game da rukunnai dabam dabam na masu amfani da wuta da abin da za su biya a matsayin kudin wuta. A yi mun ƙarin bayani a kan wadannan rukunnai. Menene ya sa dole sai an kasa al’umma zuwa rukuni -rukuni?

  • Ƙarin bayani kan yakin duniya da yadda za'a kauce wa sake barkewarsa

    30/03/2024 Duración: 20min

    Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da masu sauraro suka aiko mana ciki harda amsar tambaya da ke neman bayani a kan yakin duniya da yadda za a kauce wa aukuwar wani yakin duniya.

  • Sanadin katsewar kafofin sadarwa na Internet a nahiyar Afirka

    23/03/2024 Duración: 20min

    shirin a wannnan mako zai ba da hankali ne akan abinda ya kai ga katsewar hanyoyin sadarwa na internet a wasu sassa na Nahiyar Afirka.

  • Karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol

    16/03/2024 Duración: 20min

    Shirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa mukua wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, za mu ji karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol. Abokinku, Michael Kuduson ne ke muku lale marhabun.

  • Neman bayanni a game da mayar da kasa saniyar ware

    09/03/2024 Duración: 20min

    Kamar yadda muka saba, shirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa muku a wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayanni a game da mayar da kasa saniyar ware, da kuma tasirin haka a kan kasar da aka maida saniyar ware.

  • Amsoshin wasu daga cikin tambayoyin masu saurare daga Rfi

    02/03/2024 Duración: 20min

    A cikin shirin na wannan mako,Michael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyin,ko wadanan hanyoyi ne ake bi domin samun tikiti kujerar wakili a Kwamity tsaro na MDD.Ya kuma duba wasu tambayoyi da suka jibanci bangaren tsaro da sauren su.

  • Tarihin yan tawayen Houthi na Yemen

    17/02/2024 Duración: 20min

    A cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako, Michael Kuduson ya mayar da hankali a tambayar da ta shafi yan Tawayen Houthi na kasar Yemen.Sai ku biyo mu.

  • Tambaya da Amsa: Cikakken tarihin Hausawa 'yan asalin kasar Mali

    10/02/2024 Duración: 20min

    Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin tarihin Hausawa ‘yan asalin kasar Mali.  Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.

  • Ko me ya sa gwamnonin jihohi a Najeriya ba su da iko a kan jami’an tsaro?

    03/02/2024 Duración: 20min

    Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ yana kawo muku amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana ne, kuma duk mako yake zuwa muku a daidai wanna lokaci, kuma a wannan tasha. Ko me ya sa gwamnonin jihohi a Najeriya ba su da iko a kan jami’an tsaro? Wannan tambayar na daya daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau. Sai ku kasance tare da abokinku, Michael Kuduson.

  • Neman karin bayani a kan Somaliland da ko kasa ce mai ‘yanci?

    27/01/2024 Duración: 20min

    Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ yana zuwa muku ne da amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da wsu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako ya ke zuwa muku a daidai wannan lokaci.Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman karin bayani a kan Somaliland da ko kasa ce mai ‘yanci. Sai a biyo

  • Bayani a kan ramukan sararin samaniya (Black Holes)

    20/01/2024 Duración: 19min

    Kamar yadda aka saba, shirin yana kawo muku amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko  mana ne, kuma duk mako  yake zuwa muu a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa, akwai wadda ke neman bayani a kan ramukan nan da ke sarari, wadanda ake kira ‘black holes. 

  • Dalilan da suka hana kasashe masu tasowa dogaro da kansu a bangaren tsaro

    16/12/2023 Duración: 19min

    Shirin ‘Tambaya Da Amsa ‘ yana zuwa muku ne kowane mako a wannan tasha, inda ya  ke kawo amsoshin tambayoyin da suka samu shiga daga masu sauraronmu. Daga cikin tambayoyi da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayani a kan dalilin da ya sa kasashe masu tasowa ba iya dogaro da kan su wajen yaki da matsalar tsaro,, musamman ma ta’addanci da sauransu.

  • Bayani a kan masu 'kujerar naki' a Majallisar Dinkin Duniya

    18/11/2023 Duración: 20min

    Shirin 'Tambaya Da  Amsa' na wannan mako kaamar kowane mako, ya kawo muku tambayoyi ne da masu sauronmu suka aiko  mana, inda  ya samar da amsoshinsu daidai gwargwadon iko. Daga cikin tambayoyin da muka amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin yadda aka yi wasu kebabbun kasashe suka samu "kujerar naki' a Kwamitin Tsaro nna Majalisar Dinkin Duniya.

  • Tambaya dangane da bayani a kan kisan kare dangin Holocaust

    11/11/2023 Duración: 20min

    Tambaya daga Alhaji Haruna Kira da  Umar Ladan Baturiya daga jihar Jigawa Najeriya. So suke a banbanta  musu tsakanin ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga. Ko akwai dokar da ke hana amfani da karfi fiye da kima a kan irin wadannan masu aikata manyan laifuka?

  • Amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraron RFI

    04/11/2023 Duración: 20min

    Me ake nufi da karbar rance na biliyoyin daloli don tallafa wa naira kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yanzu ta  yi. Mataki ne mai fa’ida? Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ ne ke zuwa ma mai sauraro daga sashen Hausa na Radio France Internationale RFI. Ana iya aiko da tambayar da ake da ita ta adireshinmu na imel a rfihausatambayoyi@gmail.com .

página 1 de 2