Bakonmu A Yau
Ƙungiyar Amnesty ta zargi sojojin Najeriya da kashe ƴan-sa-kai a Zamfara
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:04:15
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya ta yi zargin cewa jirgin sojin saman ƙasar ya yi ruwan bamai-bamai kan jami’an sakai tare da kashe akalla 20 da jikkata wasu da dama a ƙauyukan Maraya da Wabi da ke ƙaramar hukumar Maru na jihar Zamfara. Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar jiya Litinin, ta ce lamarin kai tsaye ya shafi jami’an sakai da suka taru domin tunkarar ƴan bindiga da suka kai hare-hare a ƙauyukan nasu ranar Asabar. A tattaunawarsa da Ahmad Abba, Daraktan Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sunusi, ya fara da bayani kan yadda lamarin ya auku.