Bakonmu A Yau

Najeriya na shirin shigar da shanu daga Denmark

Informações:

Sinopsis

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da shirinta na shigar da wasu shanu daga ƙasar Denmark, a ƙoƙarinta na rage kashe kuɗaɗen shigar da madara da kuma wadatarta a ƙasar, wanda yawansu ya kai dala biliyan 1.5 duk shekara. Duk da ikirarin kasancewarta ƙasar da ta fi kowacce yawan shanu a nahiyar Africa, amma Najeriya na samar da tan dubu 700 na madara duk shekara ne, ƙasa da tan miliyan 1.6 da ƴan ƙasar ke buƙata. To sai dai a zantawarsa da RFI Hausa, sakataren Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya Baba Usman Ngerzelma ya ce babu buƙatar ɗaukar wannan mataki da za’a mayar da hankali kan shanun da ake da su a ƙasar.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Rukayya Abba Kabara..........