Ilimi Hasken Rayuwa

Matsin rayuwa na barazanar gurgunta karatun ƙananan yara a Najeriya

Informações:

Sinopsis

Shirin ''Ilimi Hasken Rayuwa'' tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan yadda halin matsin rayuwa ke yin tasiri a kan karatun yara ƙanana lamarin da ya sa kaso mai yawa daga cikinsu ba sa samun cikakkiyar fahimta a kan darussan da ake koya musu, saboda dalilai da dama masu alaka da matsin rayuwar. Baya ga batun ci a koshi dai, yanyayin da yara ƙanana ke tafiya makarantunsu a yanayin da ake ciki ma lamari ne da ya kamata a mayar da hankali akai, la’akari da cewar a wasu lokutan ɗan hakin da ka raina kan tsone maka ido.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.