Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare
Ra'ayoyin masu sauraro kan harajin yin wa'azi da ƴan bindiga suka sanya a Kebbi
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:10:00
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
A Najeriya wata ƙungiyar ta'addanci da ba’a kai ga tantace wa ba, ta buƙaci a’ummar Utono ta ƙaramar hukumar Ngaski a jihar Kebbi da ta biya su zunzurutun ƙudi har Naira miliyan 100, kafin su bai wa malamai damar gudanar da Tafsiri ko wa’azi a wannan watan Azumi na Ramadana. Ƴan ta'addar sun bayyana bukatar ne a wata rubutacciyar wasika da suka aika garin na Utono. Wannan dai shine karon farko da wata ƙungiya da bukaci malamai biyan wani kudi domin gabatar da wa’azi, ko da ya ke al’umma a wasu yankunan sun saba biyan kudi don neman yancin walwa, ko ayyukan noma ko ma girɓi. Yaya kuke kallon wannan sabon bukata na ƴan ta‘adda? Latsa alamar sauti don sauraren shirin...