Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Yadda wasu fitattun ƴansiyasa a Najeriya suka kafa wani sabon ƙawance

Informações:

Sinopsis

Wasu fitattun ƴansiyasa a Najeriya, sun sanar da kafa wani sabon ƙawance da zummar ƙwace mulki daga hannu shugaba Bola Tinubu a shekara ta 2027. To sai dai abin lura a nan shi ne, waɗanda suka ƙulla ƙawancen mutane ne da suka taɓa riƙe muhimman muƙamai ƙarƙashin gwamnatoci daban-daban ciki har da ta APC. Abin tambayar shine, ko waɗanne irin alƙawura ne da za su sake gabatar wa 'yan ƙasar domin samun ƙuri’aunsu? Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.