Lafiya Jari Ce

Mutane na ɓoye cutukan ƙwaƙwalwa saboda fargabar alaƙantasu da hauka

Informações:

Sinopsis

Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba na musamman kan cutuka ko kuma lalurar ƙwaƙwalwa, dama rabe-rabenta baya ga nazarin yadda mutane ke ɓoye irin wannan lalura saboda kunyar kar a alaƙanta su da ciwon hauka. Alƙaluman hukumar lafiya ta duniya WHO a shekarar 2017 sun nuna cewa kashi 19 na yawan al’ummar duniya na fama da matsalar ƙwaƙwalwa walau a babban mataki ko kuma a mataki na ƙasa, matsalar da kuma bayanan hukumar ke cewa yafi tsananta a ƙasashe masu tasowa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.