Lafiya Jari Ce

An samu ɓullar cutar sankarau a wasu jihohin arewacin Najeriya

Informações:

Sinopsis

Shirin 'Lafiya Jari Ce'  na wannan makon ya mayar da hankali ne akan cutar sankarau, wanda ke yin ƙamari a cikin yanayi na zafi da ake ciki, musamma a ƙasashenmu na nahiyar Afrika. Tuni aka samu ɓullar cutar sankarau a sassa daban-daban na Najeriya inda ta kashe gomman mutane a jihohin Kebbi da Sokoto, wadda aka bayyana ta da annoba. Masana a ɓangarorin lafiya da kuma yanayi, na ci gaba da gargaɗi kan yiwuwar ɓullar tarin cutuka sakamakon tsananin zafin da ake fuskanta a wasu daga cikin jihohin Najeriya, a wani yanayi da ake ci gaba da azumin watan Ramadana,, wannan shi ne maudu’in da shirin lafiya jari ce na wannan mako zai mayar da hankali akai sai ku biyomu.