Lafiya Jari Ce

Ƙarancin magungunan kuturta da abubuwan da ke haddasa cutar

Informações:

Sinopsis

A wannan makon shirin na lafiya jari ce ya mayar da hankali kan cutar kuturta ko kuma Lebrosy ko albaras, cutar da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ke ganin sam bai kamata a samu ɓirɓishinta a banƙasa ba.Rayuwar masu wannan lalura ta kuturta rayuwa ce mai cike da ban tausai, musamman waɗanda ke killace a asibitin na Bela wanda Turawan mishan daga Netherlands suka samar tun a shekarar 1928 wato tun gomman shekaru kafin ƴancin Najeriya. Alƙaluma sun nuna cewa, duk shekara Najeriya na ganin fiye da mutum dubu guda sabbin kamuwa da wannan cuta ta kuturta wadda tuni ta zama tarihi a wasu sassa na duniya.Masu lalurar ta kuturta na rayuwa cikin yanayi na tsangwama ko ƙyama wannan dalili ya sanya da dama daga cikinsu tattarewa a  Bela.