Wasanni

Matsalar alƙalanci na barazana ga ƙimar gasar La liga a Spain

Informações:

Sinopsis

Shirin ''Duniyar Wasanni'' tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matsalolin alƙalanci ke ƙoƙarin yin illa ga gasar La liga guda cikin manyan lig-lig biyar da aka fi ji da su a nahiyar Turai, la’akari da irin zaratan ƙungiyoyi da kuma ƴan wasa dama masu horaswar da ke fafatawa a cikinta tsawon lokaci. A bana, salon alƙalanci a gasar ta La Liga na ɗaukar hankali, musamman ganin yadda alkalai ke bayar da katin gargaɗi da kuma na kora babu ƙaƙƙautawa, alal misali anga yadda a wasanni 23 zuwa 24 da ƙungiyoyin da ke fafatawa a gasar  suka yi a wannan kaka, an bada kafin gargadi sama da dubu daya da 136, sai kuma na kora.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......